"Mambonin kwamitin sulhun MDD sun bayyana rashin jin dadinsu da kuma sakon jajantawa da ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma mutanen Guinea da tawagar ta MINUSMA," in ji sanarwar UNSC.
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da duk wani yunkuri da ya shafi tsarawa, aiwatarwa da kuma daukar nauyi dukkan hare-hare kan dakarun wanzar da zaman lafiyar na MINUSMA duba da irin namijin kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a karkashin yarjejeniyar kwamitin sulhun MDD. (Ahmad Fagam)