in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Tanzania: Tarukan majalissun kasar Sin na da babban tasiri ga duniya
2019-03-04 11:51:09 cri

Kafin bude "Taruka 2" na wannan shekara, wato taron majalisar ba da shawara han harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da na majalisar wakilan jama'ar kasar NPC, an tattauna da Humphrey Polepole, magatakardan jam'iyyar juyin-juya hali ta kasar Tanzania CCM, wadda ke rike da ragamar mulkin kasar, kan fahimtarsa game da "Tarukan 2" na kasar Sin. Yayin tattaunawar a ofishinsa dake Dar es Salaam, jami'in ya kuma furta cewa, bude tarukan 2 za ta haifar da babban tasiri ga ci gaban kasar ta Sin, kuma suna da ma'ana sosai ga sauran kasashe daban daban. Sa'an nan jami'in ya kara da cewa, yana fatan ganin bude tarukan 2 a bana za ta taimakawa kasar Sin karfafa sakamakon da ta samu a fannin raya kasa, sa'an nan ta kara samun wasu manyan ci gaba a fannoni daban daban.

Mista Polepole ya kuma bayyana burinsa game da "Tarukan 2" na kasar Sin na wannan karo, inda ya ce, kasar Tanzania muhimmiyar abokiyar kasar Sin ce a nahiyar Afirka, wadda ke da huldar hadin gwiwa na kut-da-kut da kasar ta Sin, saboda haka yana fatan ganin a wajen "Taruka 2" na bana, manyan kusoshin kasar Sin mahalartar tarukan, za su tattauna yiwuwar samar da sabbin matakai karkashin laimar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, don kara habaka ayyukan hadin kai a kasashe masu alaka da shawarar, ciki har da kasar Sin, da kasar Tanzania, gami da ba su damammakin kyautata huldarsu, da habaka hadin gwiwarsu zuwa karin fannoni.

Jami'in na kasar Tanzania ya kara da cewa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta shafi ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, da raya aikin jinya, da ilimi, da dai sauransu. Sa'an nan bisa tsarin shawarar, ana kokarin tabbatar da moriyar dukkan bangarori, da tsayawa kan neman samun ci gaba tare da kiyaye zaman lafiya. A cewar jami'in, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" wata shawara ce mai matukar kyau, domin bisa shawarar ana lura da moriyar ko wace kasa. A ganinsa, za a iya kallon shawarar a matsayin wata muhimmiyar dabara ta gina wata al'ummar dan Adama mai kyakkyawar makomar ta bai daya. Ban da haka kuma, jami'in ya ce kasarsa ta Tanzania tana rungumar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da hannu biyu-biyu, ganin yadda tushen shawarar shi ne hadin gwiwa don samun ci gaba, gami da kokarin karfafa zumunta.

Ban da haka, yayin da Humphrey Polepole, magatakardan jam'iyyar CCM mai mulki a kasar Tanzania, ke hira da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya ambaci ci gaban da kasar Sin ta samu bayan da ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, inda ya ce, ci gaban da kasar Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar ya ba ta damar fitar da jama'arta da yawansu ya kai fiye da miliyan 700 daga kangin talauci, adadin da ya kasance kashi 70% na yawan al'umma masu fama da talauci da aka rage a duniya. "Hakan wani babban ci gaba ne na a zo a gani". Ya kara da cewa, fasahohin da kasar Sin ta samu, da matakan da kasar ta taba dauka a fannin rage talauci, sun cancanci yabo, kuma ya kamata kasar Tanzania da sauran kasashen dake nahiyar Afirka su yi kokarin koyon fasahohin kasar ta Sin a wannan fanni.

Haka zalika, mista Polepole ya ce, sauran abubuwan da kasar Sin ke da su wadanda ya kamata kasashen Afirka, ciki har da Tanzania, su koya, sun kunshi dabarun kasar a fannin gudanar da mulki. "Wani muhimmin abun da ya kamata a lura da shi shi ne kokarin tabbatar da dorewar manufar gwamnati", in ji jami'in. Ya ce, wasu ayyuka, misali kyautata zaman rayuwar jama'a da kuma rage talauci, na bukatar a rika zuba musu jari na tsawon lokaci, saboda haka yadda za a iya kiyaye dorewar manufar da gwamnati ta dauka yana da muhimmanci kwarai.

Ban da haka, jami'in ya ce kasar Tanzania da kasar Sin suna da ra'ayi daya a fannin raya kasa, wato dukkansu suna sanya moriyar jama'a sama da komai. Ya ce, duk jam'iyyar dake mai da hankali kan moriyar jama'a, ita kadai za ta iya jagorantar kasa da jama'a wajen neman ci gaban da walwala. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China