in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu aikin gine-gine na Sin da Najeriya sun yi kokarin kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan
2019-02-12 15:27:28 cri

Yayin da ake taya murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a kwanakin baya, masu aikin gine-gine na Sin da Najeriya suna ci gaba da kokarin aiki tare kamar yadda ake yi a yau da kullum wajen shimfida layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan. Kawo yanzu dai, an riga an kammala wasu ayyukan shimfida layin dogon. A ranar 8 ga wata, ministan kula da sufuri na Tarayyar Najeriya Rotimi Amaechi da sauran manyan kusoshin gwamnatin kasar, suka shiga jirgin kasar, inda su da mazauna wurin suka yaba da rancen kudin da gwamnatin kasar Sin ta samar da matukar kokarin aikin da kamfanin kasar Sin ke yi.

Layin dogo a tsakanin Lagos zuwa Ibadan wani muhimmin bangare ne na aikin zamanintar da layukan dogo a Tarayyar Najeriya, wanda zai taso daga Lagos, birni mafi girma da ke bakin teku na kasar, har zuwa birnin Ibadan, hedkwatar jihar Oyo, wanda ya shahara ta fuskar masana'antu. Tsawon layin dogon ya kai kilomita 156.8, wanda aka gina bisa ma'aunin fasahar kasar Sin. Ana sa ran saurin tafiyar jirgin kasa a layin dogon zai kai kilomita 150 a ko wace awa. Jimillar kudaden da aikin ya lakume za ta kai dala biliyan 1 da miliyan 581. Bankin shige da fice na kasar Sin ne ya samar da yawancin rancen kudi mai gatanci. Ana sa ran kammala aikin wanda aka kaddamar a ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2017, cikin shekaru uku. Bisa bukatar kara saurin aikin da Najeriya ta gabatar, an riga an kammala shimfida layin dogo na kimanin kilomita 60 da ke cikin jihar Ogun da ke kusa da Lagos a farkon shekarar bana.

Wang Junhe, mataimakin manajan kula da aikin shimfida layin dogo tsakanin Lagos zuwa Ibadan da ke kamfanin CCECC ya bayyana cewa, akwai ma'aikata Sinawa kusan 700 da ma'aikata 'yan Najeriya kusan 8000 dake aikin, yayin da ake fama da aikin kuwa, yawan ma'aikata ya zarce 10000, lamarin da ya samar da guraban aikin yi da yawa ga mazauna wurin. Wang Junhe ya kara da cewa,

"lokacin gudanar da aikin ya yi kadan, ba mu yi hutu ko kadan ba yayin bikin bazara, har ma mun kara tsawon lokacin aikinmu na ko wace rana. Muna kokarin kara saurin shimfida layin dogon yayin da muke tabbatar da inganci da tsaron aikin. Iyalanmu ma sun fahimci yadda muke fama da aikin, inda nake musu fatan alheri a sabuwar shekara."

A ranar 8 ga wata, ministan kula da sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amousun, da sarkin wurin Oba Adedontun Aremu Gbadebu da dai sauran manyan kusoshin kasar suka shiga jirgin kasan don gwajin tafiya a kan layin dogon. Yayin da ake tafiya a cikin jirgin kasan, Mr. Amaechi ya shaidawa wakilinmu cewa,

"Aikin ya samar da alfanu sosai, wannan na da matukar muhimmanci. Muna ma gwamnatin kasar Sin godiya da ta samar mana rancen kudi. Aikin ya kawo mana guraben aikin yi, aikin rarraba kayayyaki, da karuwar moriya, da raguwar tsawon lokacin tafiya da dai sauransu. Ban da wannan kuma sufurin jirgin kasa ya rage nauyin hanyoyin mota wajen tafiyar manyan motocin dakon kaya, lallai mun amfana sosai."

Ban da Mr. Amaechi, mazauna wurin da ke kusa da layin dogon, su ma sun gamsu da layin, ciki har da wani mai suna Adedoiapodu Rpiado. Wanda idan ya tsaya a kofar gidansa, zai iya ganin layin dogon, ya ce,

"Lallai ina jinjina aikin da kamfanin CCECC ke yi a Najeriya. Dimbin mazauna wurinmu na samun abun yi cikin aikin shimfida layin dogon, har ma sun samu damar kasuwanci. Bayan layin dogon ya fara aiki, zai kara habaka kasuwanci. Ban da wannan, za a saukaka tafiyarmu, alal misali, da na sayi tikiti, zan iya zuwa sauran jihohi ta jirgin kasa."

An labarta cewa, layin dogo a tsakanin Lagos da Ibadan, shi ne layin dogon zamani na biyu da kamfanin CCECC ke kulawa da shi a Najeriya, ban da layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna wanda ya fara aiki a watan Yuli na shekarar 2016. Idan aka kammala layin dogon, zai sa kaimi ga raya albarkatu da tattalin arzikin yankunan da layin ya shafa, da ma taimaka wajen raya masana'antu, har ma ana sa ran za a kyautata matsalar "shan wahalar tafiye-tafiye da samun yawan hadarorin mota" da Najeriya ke fuskanta. Lallai aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen raya kasar Najeriya da kyautata zaman rayuwar jama'arta. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China