in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karon farko shugaba Xi Jinping ya gana da wakilan tattalin arziki da kasuwanci na kasar Amurka
2019-02-16 09:11:00 cri

A jiya Jumma'a ne manyan jami'an kasashen Sin da Amurka suka kammala zagaye na shida na tattaunawar da suke yi kan harkokin tattalin arziki da cinikayya, taron da ya gudana daga Alhamis zuwa Jumma'a a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da jami'an gwamnatin Amurka da suka jagoranci tawagar ta Amurka a taron na kasar Sin, ciki har da wakilin kasuwancin kasar Robert Lighthizer da sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin, inda ya jaddada cewa, Sin da Amurka ba za su iya rabuwa da juna ba, kana, hadin-gwiwa shi ne abu mafi kyau a gare su. Shugaba Xi yana kuma fatan tawagogin kasashen biyu za su kara tuntubar juna, da maida hankali kan karfafa hadin-gwiwa da daidaita sabanin ra'ayi tsakaninsu, a wani mataki na ciyar da hadin-gwiwar dake tsakaninsu ta fannin tattalin arziki da cinikayya gami da dangantakarsu gaba.

Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan Amurka ta bangaren tattalin arziki da cinikayya tun tsanantar takaddamar cinikayya tsakanin kasashen biyu a watan Fabrairu din bara. Hakan na nufin cewa, an kara samun babban ci gaba a shawarwarin wannan zagaye bayan da aka samu muhimmin ci gaba a yayin shawarwarin da suka gudanar a birnin Washington na Amurka makwanni biyu da suka shige.

Manazarta na ganin cewa, a yayin da ya sha ganawa da wakilan kasar Amurka, Xi Jinping ya ambaci kalmar "hadin-gwiwa", abun da ya shaida irin niyya gami da sahihancin da kasar Sin take da su wajen daidaita matsalar kasuwanci tare da Amurka ta hanyar yin hadin-gwiwa. Xi ya kuma ce, "hadin-gwiwa na da sharadi", wato tushen hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da kasuwanci shi ne, kiyaye manyan muradun kasa gami da hakkokin al'ummarta.

Tun lokacin da takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ta tsananta a watan Fabrairu din bara, ya zuwa yanzu, hira ta waya sau biyu gami da tattaunawa sau daya da shugabannin kasashen biyu suka yi, sun taka muhimmiyar rawa wajen sassauta rikici a tsakaninsu. Musamman a yayin ganawarsu a kasar Argentina a watan Disambar bara, shugabannin Sin da Amurka sun cimma matsaya a wasu muhimman fannoni, ciki har da dakatar da kara bugawa juna haraji, lamarin da ya sauya yanayin da ake ciki na fuskantar tsanantar takaddamar ciniki.

A watanni uku da suka gabata, sakamakon matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tawagogin ma'aikatan tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka suna kara tuntubar juna da gaggauta yin shawarwari, don daidaita matsalar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu. Bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan wasu muhimman batutuwa dake shafarsu, ciki har da musayar fasahar kere-kere, kare 'yancin mallakar fasaha, da matakan takaita shigo da kayayyaki da ba'a biya musu haraji, da fannonin samar da hidima, aikin gona, daidaiton cinikayya da yadda za'a aiwatar da matakan da aka cimma da kuma batutuwan da suka shafi kasar Sin. Bangarorin biyu za su ci gaba da himmatuwa wajen kara cimma maslaha tsakaninsu, da ci gaba da yin shawarwari a makon gobe a birnin Washington na kasar Amurka.

Wannan ya shaida cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan batutuwan da suka maida hankali kansu, kana sun cimma daidaito kan manyan batutuwa, lamarin da ya sa bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa da kuma warware matsalolinsu sannu a hankali. Batutuwan da suka cimma daidaito sun shaida aniyyar kasashen biyu baki daya, wanda ya shaida ka'idojin nuna daidaito da samun moriyar juna a tsakaninsu.

Sin da Amurka sun tattauna kan yadda za su amince da takardar fahimtar juna kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya a yayin shawarwarin, wannan ya shaida cewa, an shiga matakin tsaida yarjejeniyar shawarwarin, wannan wani muhimmin ci gaba ne. Game da batun tsarin gudanar da ayyuka da bangarorin biyu suka cimma, a sakamakon cimma daidaito kan tsari da ka'idoji a yayin shawarwarin Washintgon, za kuma a kara yin tattaunawa kan wannan batu a shawarwarin a wannan karo, wannan zai taimaka wajen tabbatar da aiwatar da matakai da suka cimma daidaito a kai.

Abin mafi jawo hankali shi ne tawagogin tattalin arziki da cinikayya ta Sin da Amurka za su ci gaba da yin shawarwari a mako mai zuwa a birnin Washington na kasar Amurka. Wannan ya shaida cewa, Sin da Amurka suna begen cimma yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu a cikin lokacin da aka tsara. A ganawarsu da shugaba Xi Jinping, Mr. Lighthizer da Mr. Mnuchin sun bayyana cewa, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu sun cimma babban ci gaba a manyan batutuwa, ko da yake akwai ayyuka da dama da za a gudanar, amma suna nuna kyakkyawan fata na cimma burinsu yadda ya kamata.

Akwai matsaloli da dama a fannonin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, kuma zai yi wuya a warware su a cikin kwanaki 90. Amma tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Amurka za su ci gaba da yin mu'amala da juna da ci gaba da yin shawarwari a mako mai zuwa, kana shugabannin kasashen biyu sun gana da wakilan tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu, har ma kasar Amurka ta bayar da labari cewar shugabannin kasashen biyu za su sake ganawa, don haka kasashen biyu na nuna kyakkyawan fata na cimma yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta yadda za a samu moriyar juna a tsakaninsu.

A cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin da Amurka sun fuskanci matsalolin fahimtar juna saboda bambancin tsarinsu da tarihi da al'adunsu da kuma yanayinsu. A karshe, shugabannin kasashen biyu sun yi kokarin ganin an daidaita matsalolin kasashen biyu cikin nasara, kana za a kara fahimtar juna da kuma sa kaimi ga raya dangantakar hadin gwiwarsu yadda ya kamata. Don haka, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da hada kai da kara yin hadin gwiwa da juna da kuma shawo kan fannonin da suke da bambancin ra'ayoyi, hakan zai taimaka wajen warware matsalolinsu da samar da damar samun moriyar juna.(Murtala Zhang, Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China