in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gamsu da matakin Amurka na jingine batun amfani da karin haraji
2019-03-02 15:44:06 cri
A yau Asabar, kwamiti mai kula da ka'idojin haraji karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce ya samu wata sanarwa da ofishin wakilin Amurka mai kula da batun cinikayya ya gabatar, inda aka ce ba za a kara karbar haraji kan wasu kayayyakin da ake shiga da su kasar daga kasar Sin ba, wadanda a baya aka ce za a karbi karin haraji kan su daga watan Satumban shekarar 2018. Abun nufi shi ne, za a ci gaba da amfani da harajin yanzu na kashi 10% na darajar kayakin, har zuwa wani lokacin da ake da bukatar gyara tsarin. Dangane da haka ne, kwamitin na kasar Sin mai kula da ka'idojin haraji na majalisar gudanarwar kasar, ya ce ya gamsu da matakin da bangaren Amurka ya dauka. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China