Wang Xiaohui, mataimakin darektan sashin kula da fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, yana gwada fasahar nuna bidiyon na 4K ta wayar salula mai fasahar 5G.
Shen Haixiong, mataimakin darektan sashin kula da fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kamfanin CMG, yana jawabi.
Bikin kaddamar da gwajin fasahar 5G.
Yayin da ake jiran bude tarukan majalissun kasar Sin cikin wasu kwanaki, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya gwada tsarin watsa labarunsa ta hanyar amfani da sabuwar fasahar sadarwa ta 5G a yau Alhamis, inda aka watsa shirin bidiyo mai inganci bisa tsarin 4K.
An gudanar da gwajin ne, ta hanyar daukar hoton bidiyo bisa tsarin 4k, sa'an nan aka tura bidiyon zuwa dakin gwajin fasahar 5G na CMG, daga bisani aka watsa bidiyon ta wani nau'in wayar salula da kamfanin Huawei na kasar Sin ya kera. Wannan gwajin ya nuna cewa, dakin gwajin fasahar 5G na CMG ya bullo da wata fasahar karbar bidiyo na 4k, sannan ya hada su a matsayin shiri, ya kuma watsa shirin nan take. Rahotanni na cewa, za a fara yin amfani da wannan sabuwar fasaha wajen watsa labaru da rahotanni da suka shafi tarukan majalissun kasar Sin na bana. (Bello Wang)