Jami'in ya kara da cewa, a wannan karon kasashen Canada da Amurka sun yi amfani da dokarsu ta tasa keyar wanda ya aikata laifi ba tare da kima ba. Sa'an nan tsare wani Basine ba tare da hujja ko dalili ba, keta hakkin dan Adam ne. Lamarin da a cewar jami'in, babban batu ne a fannin siyasar duniya.
Lu Kang ya kara da cewa, kasar Sin ta sake kalubalantar bangaren Amurka da ya soke sammacin Madam Cathy Meng, sannan ta bukaci Canada da ta sake ta ba tare da wani jinkiri ba.(Bello Wang)