in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: ya kamata a tabbatar da raya aikin sadarwa cikin adalci ba tare da rufa-rufa ba a duniya
2019-02-27 11:27:57 cri

Wakilin kasar Sin ya yi kira ga masana'antun aikin sadarwa na kasa da kasa da su yi kokari tare wajen tabbatar da raya aikin sadarwa cikin adalci ba tare da rufa-rufa ba.

Zhang Feng, babban injiniyan ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ne ya bayyana haka jiya Talata, yayin babban taro kan aikin sadarwa na duniya. Zhang Feng ya kuma ce, a halin yanzu da ake raya tattalin arzikin duniya baki daya, jerin sana'o'i na fasahar 5G daban daban, na kara azama kan yin takara yadda ya kamata, tare da bai wa kamfanoni karin zabi, da kuma kara bai wa jama'a hidima mai kyau.

Zhang Feng ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa haikan wajen bude kofa ga waje da yin hadin gwiwa da kasashen duniya, da kokarin samar da yanayi mai kyau wajen raya masana'antun fasahar 5G, da hada kai da kamfanonin fasaha na duniya da abokan hadin gwiwa na kasa da kasa da kuma kungiyoyin duniya, wajen bunkasa fasashar 5G ta hanyar kirkire-kirkire.

An bude babban taron aikin sadarwa na duniya na shekarar 2019 ne a ranar 25 ga wata a birnin Barcelona na kasar Spaniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China