Mambobin kwamitin sulhun MDDr sun bayyana sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ta ranar 6 ga watan Fabrairu a babban birnin kasar Bangui da cewa, wani muhimmin mataki ne wajen samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a CAR da kuma samun cikakken tsarin shugabanci a kasar, in ji sanarwar.
Mambobin MDDr sun bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a CAR da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da kyakkyawar zuciya kuma ba tare da jinkiri ba. Kana mambobin sun bayyana muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa adalci da kuma ba da cikakkiyar dama ga kungiyoyin fararen hula, da mata da matasa cikin shirin zaman lafiyar.
Haka zalika kwamitin MDDr, ya bukaci dukkan kungiyoyin masu dauke da makamai da su kawo karshen dukkan tashe-tashen hankula da gallazawa fararen hula, da jami'an kiyaye zaman lafiya, da masu bayar da tallafin jin kai, kuma su guji wargaza hanyoyin zaman lafiya, kana su baiwa jami'an bayar da agajin jin kan al'umma damar shiga wuraren bayar da tallafin da kuma bai jama'a 'yancin walwala. (Ahmad Fagam)