Bangarorin uku sun bayyana cewa, a matsayinsu na manyan kasashen duniya da sabbin kasashe mafiya samun ci gaban tattalin arziki a duniya, ya kamata Sin da Rasha da Indiya su kara yin hadin gwiwa bisa sauyin yanayin da ake ciki a duniya, ta hakan za a kawo tabbaci da tasiri mai kyau a duniya.
Ban da wannan kuma, bangarorin uku sun cimm daidaito kan tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban, da kara yin mu'amala da juna bisa tsarin bangarori daban daban, da yaki da ta'addanci tare, da kin amincewa da ra'ayin bangare daya, da bada kariya ga cinikayya, da warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari, da sake yin ganawar dake tsakanin shugabannin kasashen uku, da fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasashen uku da saurausu. (Zainab)