in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi tsokaci kan ziyararsa a kasashe 4 na Afirka
2019-01-07 11:21:29 cri
A ranar 6 ga wata, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai kawo karshen ziyararsa a kasashe 4 na Afirka, ya bayyana ra'ayinsa game da ziyararsa ga 'yan jarida a birnin Dakar.

Wang Yi ya ce, kullum ministan harkokin wajen kasar Sin yana kai ziyararsa ta farko ne a nahiyar Afirka a kowace shekara, wannan wani muhimmin al'amari ne a harkokin diplomsiyya na kasar Sin. Dalilin da ya sa aka yi hakan har na tsawon shekaru fiye da 10 shi ne Sin ta yi alkawari ga Afirka, kana Sin da kasashen Afirka dukkansu kasashe ne masu tasowa, su abokai ne masu nuna goyon baya ga juna da warware matsaloli tare. Ana bukatar bangarorin biyu su kara yin mu'amala da hadin gwiwa mai zurfi. Ya bayyana ra'ayinsa game da ziyararsa a wannan karo.

Na farko shi ne ana sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka har abada. Na biyu shi ne dukkansu suna nuna goyon baya ga ra'ayin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. Na uku shi ne suna son kara raya shawarar "ziri daya da hanya daya" tare. Na hudu kuma shi ne ana tsayawa tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak a duniya a nahiyar Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China