in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Kasar Sin za ta kara raya ayyukan diplomasiyya a shekarar 2019
2019-02-01 10:58:58 cri
Mamban kwamitin gudanarwa na kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Mr. Wang Yi, ya bayyana cewa, a wannan sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin shugaba Xi Jinping kan harkokin diplomasiyya, ta yadda harkokin za su kai wani matsayi.

Mr. Wang Yi ya yi wannan furuci ne jiya a birnin Beijing, a gun liyafar da aka shirya wa jakadun kasashen waje da ke kasar Sin da ma wakilan kungiyoyin duniya da ke kasar don sabuwar shekarar 2019.

A cikin jawabin da ya gabatar, Wang ya ce, kasar Sin ba za ta nema mallakar duniya ba, kuma ba za ta yadada girmanta zuwa ketare ba, kuma kasar Sin na daukar ra'ayin kafa hulda ta sabon salo tsakanin kasa da kasa, wadda za ta mai da hankali kan girmama juna, da adalci, da ma hadin gwiwa don moriyar juna. A waje daya kuma, kasar Sin na fatan sauran kasashe za su iya zabar hanyar neman samun bunkasuwa cikin lumana yadda ya kamata.

Ban da wannan kuma, Wang Yi ya ce, a wannan sabuwar shekarar, kasar Sin za ta kokarta wajen neman samun hanyoyin warware matsaloli masu jawo hankalin mutane bisa halayyarta ta musamman.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China