in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sudan
2019-01-29 11:00:59 cri
A ranar 28 ga wata, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sudan Faysal Hassan Ibrahim Ali a nan birnin Beijing na kasar Sin.

Faysal ya yi bayani game da halin da ake ciki a kasar Sudan, inda ya bayyana cewa, an shawo kan halin da ake ciki a kasar, tare da mayar da zaman rayuwar jama'ar kasar yadda ya kamata. Kasar Sudan ta ki amincewa sauran kasashe su tsoma baki kan harkokin cikin gidanta. Ya jaddada cewa, kasar Sudan tana godiya ga kasar Sin domin yadda ta samar mata da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da sa kaimi ga raya tattalin arziki a dogon lokaci. Ya ce, kasar Sudan tana son koyon fasahohin samun bunkasuwa na kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin bisa tsarin shawarar "ziri daya da hanya daya", da yin maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari ga kasar, kuma Sudan za ta ci gaba da nuna goyon baya ga matsayin Sin mai dacewa kan harkokin kasa da kasa.

A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, a matsayinta na kawar kasar Sudan, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar wajen bin hanyar samun bunkasuwa mai dacewa da yanayinta, da tabbatar da zaman lafiya, da kuma kin amincewa bangarorin waje tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasa. Ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu su tattauna sabbin hanyoyin yin hadin gwiwa a tsakaninsu, da kara hada kan juna bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da tsarin shawarar "ziri daya da hanya daya", da kuma raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi ta hanyar yin amfani da damar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China