in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin tana fatan ziyarar Wang Yi za ta ciyar da alaka tsakanin Sin da Faransa da Italiya gaba
2019-01-23 20:11:41 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasar Sin tana fatan ziyarar da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai yi a kasashen Faransa, da Italiya, za ta ciyar da alakar dake tsakanin kasar Sin da wadannan kasashen biyu gaba yadda ya kamata, ta yadda za ta kai ga wani sabon matsayi.

Wang Yi ya tashi ne yau daga nan birnin Beijing, zuwa kasar Faransa, domin halartar taron manyan jami'ai masu jagorancin tattaunawa tsakanin sassan biyu, bisa manyan tsare-tsare, daga baya kuma zai kai ziyara kasar Italiya, tare kuma da shugabantar taron kwamitin gwamnatocin kasashen Sin da Italiya karo na 9.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China