in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Akwai kyakkyawan fata gami da kalubale a shekarar 2019
2019-02-25 20:03:52 cri
Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, ya halarci wani bikin da ya gudana a nan Beijing a yau, inda ya yi jawabin cewa, akwai kyakkyawan fata gami da kalubale a duniyarmu a shekarar 2019. Ya ce a wannan makon da muke ciki, shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka za su gana karo na biyu, wadda ake fatan za ta taimaka wajen kau da makaman nukiliya daga zirin Koriya, da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a zirin. Haka zalika, an samu ci gaba a shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka kan batun tattalin arziki da ciniki, lamarin da ya sa ake sa ran ganin kyautatar hulda tsakanin Sin da Amurka, da ci gaban tattalin arzikin duniya. Amma, a cewar jami'in, ya kamata a lura da cewa, yanzu a wurare daban daban na duniyarmu ana fama da tashin hankali, da abubuwan keta ka'idojin huldar kasa da kasa. Saboda haka, kasar Sin za ta yi kokarinta, domin hadin gwiwa da kasashe daban daban, tare da burin tabbatar da kwanciyar hankali a duniyarmu. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China