in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara ba da rancen bankuna ga kamfanoni masu zaman kansu
2019-02-26 10:18:28 cri

Mahukuntan kasar Sin, sun bukaci a kara ba da tallafin kudi ga kamfanoni masu zaman kansu, suna masu bukatar manyan bankunan gwamnati su mayar da hankali wajen kara yawan rance ga kanana da matsakaitan kamfanoni.

A cewar daftarin da hukumar kula da ayyukan bankuna da inshora ta kasar Sin wato CBIRC ta fitar jita Litinin 25 ga wata, ya kamata manyan bankunan gwamnatin masu ba da rancei, su ga rance da kananan da matsakaitan kamfanoni suke karba da ya kai kudin Sin RMB yuan miliyan 10 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.5 ko kasa da haka, ya karu da kaso 30 a bana.

A shekarar da ta gabata ne kasar Sin ta kara kokarin samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga kamfanoni masu zaman kansu, domin warware matsalolin kudi da suke fuskanta tare da neman samun ci gaban tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China