in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da ka'idojin tsaurara bincike kan ingancin abinci
2019-02-25 11:22:41 cri

Kasar Sin ta bayyana muhimman ka'idojin da za'a yi amfani da su wajen karfafa bincike game da ingancin abinci a yankunan kananan hukumomin kasar.

Bisa ka'idojin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wato CPC da majalisar gudanar da mulkin kasar Sin suka fitar a karshen mako, an ce, batun ingancin abinci yana daga cikin muhimman fannonin da ake amfani da su wajen tantance aikin manyan kusoshin kasar da na jam'iyyar.

Ka'idojin za su taimaka wajen kyautata ingancin abinci da kyautata rayuwar al'umma a yankunan kananan hukumonin kasar.

Ingancin abinci, ya hada da kula da lafiyar amfanin gona, wanda za'a shigar da shi cikin tsarin raya cigaban tattalin arzikin kasa da shirin bunkasa cigaba na kananan hukumomi. Kana za'a sanya batun cikin muhimman ayyukan da za'a dora muhimmanci a kai a kananan hukumomin don tabbatar da bin doka da oda daga jami'an bada shawarwari kan harkokin siyasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China