Shirin raya yankin Guangdong da Hong Kong da Macao, ko kuma Greater Bay Area a Turance, ya zama wurin da aka fi samun kwararar kwararru, yayin da kuma yake da damar jan hankalin kwararru na kasashen waje.
A cewar wani rahoton hadin gwiwa da Jami'ar Tsinghua na kasar Sin da kamfanin LinkedIn China suka fitar, kan kwararru 439,000 da wasu wasu 118,000 dake aiki a bangaren fasahar sadarwa a yankin, Yankin na daya daga cikin wuraren da suka fi jan hankali kwararru kan fasahar zamani a kasar Sin, domin ya zarce Beijing da Wuhan a wannan bangare.
A makon da ya gabata ne kasar Sin ta fitar da wani jadawalin raya yankin Guangdong da Hong Kong da Macao, wanda ke da nufin zama wani babban birni a duniya da zai kara ingiza manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ta kasar Sin.
A cewar Wang Yanping, shugaban kula da manufofin da harkokin gwamnatin kasar Sin a LinkedIn, fahimta da amfani da albarkar yawan al'umma zai taimaka wajen kai wa ga samun ci gaba a bangarori da dama da kuma biranen yankin.
Yankin Greater Bay shi ne ke da manyan kwararru a fannonin sarrafa kayayyaki da samar da kayakin amfanin yau da kullum da fasahar sadarwa na zamani. (Fa'iza Mustapha)