Geng Shuang ya yi nuni da cewa, bisa kididdigar da hukumomin Sin da abin ya shafa suka fitar, ta nuna cewa, yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje a kasar Sin a shekarar 2018 ya kai fiye da dubu 60, wanda ya karu da kashi 69.8 cikin dari bisa na shekarar 2017. Yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a shekarar ya kai dala biliyan 135, wanda ya karu da kashi 3 cikin dari. An samu wadannan karuwa ne sakamakon zirga-zirgar mutane a tsakanin Sin da kasashen waje, ciki har da 'yan kasuwa na kasashen waje da dama da suka kawo ziyara da ma yin shawarwarin ciniki a kasar Sin. Idan kasar Sin ba ta tabbatar da tsaro ba, ba za a samu irin wannan Alkalamu ba. (Zainab)