A wannan sabuwar cibiyar, za a yi kokarin samar da sabbin fasahohi masu alaka da na'urori masu amfani da fasaha da kansu, da gwajin amfani da su. Ta haka, ana sa ran maida birnin Beijing ya zama kan gaba a duniya wajen mallakar fasahohi, da kwararru, gami da daidaituwar manufa, a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.
Da ma dai birnin Beijing yana da fifiko wajen kirkiro sabbin fasahohi masu alaka da na'ura mai kwaikwayon tunanin dan Adam, musamman ma a fannonin manufar gwamnati, kwararru, da masana'antu. Daga bisani gwamnatin wurin ta kara daukar wasu matakai cikin shekarun nan, don tallafawa sana'ar daga dukkan bangarori. (Bello Wang)