Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaransa na kasar Kyrgyzstan Chingiz Aidarbekov, wanda ke ziyara a kasar, sun gana da manema labaru bayan ganawarsu jiya Alhamis, a nan Beijing
Wang Yi ya ce, kasar Sin ta shirya taron koli a birnin Qingdao cikin nasara a watan Yunin bara, inda shugaba Xi Jinping, ya gabatar da ra'ayinsa kan bunkasuwa, harkokin tsaro, hadin gwiwa, da tafiyar da harkokin duniya. Ya kuma takaita yadda za a raya huldar kasa da kasa ta sabon salo, tare da nuna yadda za a raya kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO. Har ila yau, an cimma daidaito kan zurfafa hadin gwiwa ta fuskar siyasa, tsaro, tattalin arziki, al'adu da dai sauransu a yayin taron, wanda ya kara azama kan shiga sabon zamani na raya kungiyar SCO.
Sa'an nan kuma, ministan harkokin wajen Sin ya ce, bayan taron koli na Qingdao, Kyrgyzstan ce ta karbi shugabancin kungiyar na karba-karba, inda kuma take sauke nauyin dake wuyanta yadda ya kamata. Ya ce kasar Sin na son hada kai da Kyrgyzstan da sauran kasashe mambobin kungiyar wajen aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Qingdao, da kara azama kan raya hadin gwiwar da ke cikin kungiyar SCO a sassan daban daban zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)