Wani rahoto ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, wanda aka gabatar a taron kwamitin da'a na kawamitin tsakiya karo na 19 (CCDI) na jam'iyyar Kwaminis (CPC), wanda babban jami'in kwamitin Zhao Leji ya gabatar a ranar 11 ga watan Janairu.
Tabbatar da gina manufofin jam'iyya zai kasance muhimmin ginshiki, wanda ta haka ne za'a samu nasarar kakkabe dukkan wasu ayyukan da ba su dace ba, inji rahoto.
Tsare tsare da kuma irin matakan da ake bi wajen sanya ido za'a aiwatar da su ne domin inganta sha'anin ayyukan gwamnati baki daya, inji rahoton.(Ahmad Fagam)