in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan za a fahimci dokar leken asiri ta kasar Sin a dukkan fannoni
2019-02-19 20:37:58 cri
Game da dokar leken asiri ta kasar Sin da bangarorin kasashen waje suke nuna shakka a kai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, aya ta 7 ta dokar leken asiri ta kasar Sin ta nuna cewa, ya kamata dukkan kungiyoyi da jama'ar kasar Sin su nuna goyon baya da ba da gudummawa ga ayyukan leken asiri na kasar, da kare asirin kasar. Kana bisa aya ta 8 ta dokar, ta ce ya kamata a gudanar da ayyukan leken asiri bisa dokoki, da girmama da kare hakkin dan Adam gami da muraden mutane da ma kungiyoyi. Kakakin yana fatan wadanda ke adawa da wannan doka za su fahimci dokar yadda ya kamata, maimakon kallon ta ta bangare daya, da kuma yi mata gurguwar fahimta.

Hakazalika kuma, Geng Shuang yana fatan bangarori da abin ya shafa da su nazarci ka'idojin dokar yadda ya kamata, su kuma daina adawa da dokar ba tare da wata hujja ba, su kuma maida hankali ga ayyukan cinikayya na kamfanonin Sin cikin adalci. Kana yana fatan gwamnatocin kasashen duniya da abin ya shafa za su martaba ka'idojin kasuwa ta yin takara cikin adalci, da kuma samar da yanayi mai adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin Sin da suka gudanar da ayyuka a kasashensu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China