Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasarsa na martaba rawar da Iran ke takawa a harkokin shiryya-shiyya, tana kuma fatan za ta kara taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Wang ya bayyana hakan ne a yau Talata, yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Iran Mohammed Javad Zarif a nan birnin Beijing. Ya ce kasashen Sin da Iran kasashe ne masu tarihin dubban shekarun na wayewar kai da al'adun kana duk da canje-canjen dake faruwa a duniya, kasashen biyu, za su ci gaba da karfafa alakarsu bisa manyan tsare-tsare da kiyaye tare da karfafa alakarsu ta dogon lokaci, a kokarin bullo da sabbin abubuwa cikin hadin gwiwar dake tsakaninsu.
A nasa jawabin Zarif, ya ce, bangaren Iran yana martaba alakar dake tsakaninsa da kasar Sin, kana yana daukar kasar Sin a matsayin muhimmiya kuma aminiyar hadin gwiwa a dukkan fannoni.
Ya kuma bayyana kudurin kasarsa na shiga a dama da ita wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya, yana mai cewa, shawarar tana da muhimmanci na musamman ga kasashen na Sin da Iran.(Ibrahim)