in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikin madatsar ruwan Habasha da darajarsa ya kai sama da miliyan 40
2019-02-20 10:03:32 cri
Kamfanin gine-gine na kasar Sin, China Gezhouba Group Co.LTD wato (CGGC), ya rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangila da gwamnatin Habasha, domin shiga aikin ginin katafariyar madatsar ruwan kasar.

A yarjejeniyar ta dala miliyan 40.1, kamfanin CGGC zai shiga ayyukan da ake yi kafin a kai ga samar da makamashi daga madatsar ruwan, wadda zata zama madatsar ruwa mafi girma a nahiyar Afrika da girmanta ya kai cubic meter miliyan 74,000.

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki ta kasar, Abrham Belay, ya bayyana yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Addis Ababa cewa, ana sa ran yarjejeniyar da aka cimma da CGGC ta gaggauta aikin ginin madatsar ruwan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China