A yau ne, jiragen ruwan yaki na Amurka guda biyu suka kutsa kai cikin yankin tekun da ke tsibirran Nansha na kasar Sin. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta nuna matukar rashin jin dadinta, inda ta bukaci Amurka da ta daina irin wannan yunkuri na tayar da fitina ba tare da bata lokaci ba. A waje daya kuma ta jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki duk wani mataki da ya dace domin kare 'yancin kasar da tsaronta da ma zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudancin tekun kasar.(Kande Gao)