in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kokarin kasar Sin na haramtar safarar hauren giwa ya haifar da kyakkyawan sakamako
2019-02-19 13:09:43 cri
Al'ummomin duniya sun yabawa kasar Sin, yayin da aka fara ganin alfanun tsauraran matakanta na haramta cinikin hauren giwa.

Hukumar kula da halittun daji ta kasar kenya ta ruwaito a shafinta na Tweeter, Babban Sakataren ma'aikatar kula da yawon bude ido da halittun daji na kasar, Najib Balala na godewa ga kasar Sin bisa rufe kasuwarta ta cinikin hauren giwa da ta yi, a madadin gwamnatin kasarsa da kungiyar kawancen kasashe 32 dake rajin kare Giwaye.

Kiddidigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar, ta ce a shekarar 2018, hukumar ta kwace nau'ikan halittun dake fuskantar barazanar karewa da dangoginsu guda 25,671, ciki har da hauren giwa da nauyinsa ya kai kg 800.

Kasar Sin ta shafe shekaru tana tsaurara matakan kare hallitun daji. A ranar 31 ga watan Disamban 2017 ne aka haramta sarrafawa ko cinikin hauren giwa da dangoginsa a fadin kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China