in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan wasu kasashe 8 ta fara ziyara a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2019-02-16 15:54:15 cri
Bisa gayyatar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi, jakadu da manyan jami'an diflomasiyya na wasu kasashe 8, da suka hada da Pakistan da Venezuela da Cuba da Masar da Cambodia da Rasha da Senegal da Belarus, wadanda suke da ofisoshinsu a Genevan kasar Switzerland, sun iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a jiya Jumma'a. Jami'an za su fara ziyararsu a jihar Xinjiang dake yammacin kasar Sin ne daga yau Asabar, inda za su kammala a ranar 19 ga wata. Mataimakin shugaban sashin kula da aikin fadakarwa na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Jiang Jianguo, da mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Le Yucheng, sun gana da mambobin tawagar bayan isowarsu birnin Beijing a jiyan.

Yayin ganawar tasu, mista Jiang ya ce, tun daga shekarun 1990, wasu mutanen da suka rungumi ra'ayin ta'addanci, da kaifin kishin addinin Islama, wadanda ke neman balle jihar Xinjiang daga kasar Sin, sun kaddamar da hare-haren ta'addanci fiye da dubu 1 a jihar, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukan jama'a gami da ta dukiya masu yawa. Ya ce domin tinkarar wannan matsalar, gwamnatin jihar Xinjiang ta koyi fasahohin wasu kasashe na dakile 'yan ta'adda, gami da lura da hakikanin yanayin da ake ciki a jihar, ta yadda ta gabatar da wata dabara mai taken "mai da hankali kan ayyukan dakile ta'addanci da rigakafinsa a lokaci guda". Daga bisani kuma, aka kafa cibiyoyin koyar da ilimin sana'a, inda ake taimakawa mutane koyon yaren Sin, da ilimin shari'a da na sana'o'i, don neman kau da tsauttsauran ra'ayinsu mai alaka da addini, gami da ba su damar samun guraben aikin yi. Ya kara da cewa, matakin da aka dauka ya yi amfani, domin ya sa an daina ganin aukuwar hare-haren ta'addanci cikin watanni 25 a jere, gami da baiwa jama'ar wurin kwanciyar hankali da tsaro.

A nasu bangaren, jakadu da sauran jami'an diflomasiyya na kasashen 8 sun yaba wa kasar Sin kan turbarta ta samun ci gaba mai halayyar musamman, kuma sun nuna niyyarsu ta hadin kai da kasar a kokarin da suke na daukaka matsayin kare hakkin bil Adama a duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China