in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin zai tafi Amurka don gudanar da shawarwari
2019-02-19 10:25:35 cri
Bisa gayyatar da kasar Amurka ta yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai rike da ragamar mulkin kasar, kana mataimakin firaministan kasar, wanda kuma ke daukar nauyin jagorantar shawarwarin da ke gudana tsakanin Sin da Amurka kan tattalin arziki, mista Liu He, zai ziyarci birnin Washington na kasar Amurka, inda a tsakanin ranekun 21 da 22 ga watan Fabrairun da muke ciki, zai tattauna da Robert Lighthizer, wakilin gwamnatin kasar Amurka mai kula da batun ciniki, da Steven Mnuchin, ministan kudin kasar Amurka, lamarin da zai kasance musayar ra'ayi tsakanin manyan jami'an bangarorin Sin da Amurka kan batun tattalin arziki da cinikayya karo na 7. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China