Mahalarta ganawar sun hada da mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, kana mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS kana jagoran bangaren Sin a tattaunawar ta Sin da Amurka, da wakilin cinikayyar Amurka Robert Lighthizer da sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin.
Bangarorin biyu sun kuma aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin ganawarsu a kasar Argentina a shekarar da ta gabata, kana sun yi tattaunawa mai zurfi kan wasu muhimman batutuwa dake shafarsu, ciki har da musayar fasahar kere-kere, kare 'yancin mallakar fasaha, da matakan takaita shigo da kayayyaki da ba'a biya musu haraji, da fannonin samar da hidima, aikin gona, daidaiton cinikayya da yadda za'a aiwatar da matakan da aka cimma da kuma batutuwan da suka shafi kasar Sin.
Bangarorin biyu sun kuma amince cewa, za'a ci gaba da tattaunawar a mako mai zuwa a birnin Washington na kasar Amurka.(Ibrahim)