in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG za ta gabatar da bikin kide-kide da raye-raye na bikin kunna fitilu na shekarar 2019
2019-02-18 20:27:15 cri

A yau ne, babbar kafar rediyo da telebijin ta kasar Sin wato CMG ta gabatar da tsarin shirye-shiryen da za a gabatar gobe a bikin kide-kide da raye-raye na bikin kunna fitilu na shekarar 2019, za a gabatar da bikin ne da karfe 8 na daren ranar bikin kunna fitilu na ranar 19 ga wata. Wannan ne biki na farko da aka gabatar tun bayan da aka kafa babbar kafar watsa labarai ta CMG. A yayin bikin, za a gabatar da shirye-shiryen kide-kide da raye-raye, da wasannin ban dariya, da wasan kwaikwayo, da kuma al'adun gargajiya.

Cin mulmulallen garin shinkafa mai yauki da kallon fitilu masu launuka da amsa tambayoyin wasan kwakwalwa da aka rubuta kan fitilu n adage cikin al'adun gargajiya na bikin kunna fitilu. Bisa labarin da wanda ya rubuta yadda za a gabatar da shirye-shiryen bikin Qin Xinmin ya bayar, an ce, za a gwada wadannan al'adun gargajiya a yayin bikin, kana za a gayyaci kwararru a fannin al'adun gargajiya da wadanda suka gaji fasahohin al'adun gargajiya ba na kayayyaki ba, wadanda za su gwada yadda za a dafa mulmulallen garin shinkafa mai yauki da kwaba madi da kuma gari don yin siffofin mutane, da kuma sarrafa filitu masu launuka don murnar bikin kunna fitilu na Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China