in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG: Manyan labarai 10 na Sin a shekarar 2018
2018-12-31 20:53:38 cri
Kasar Sin ta yi babban tasiri a harkokinta na cikin gida da na kasa da kasa a wannan shekara ta 2018. Yayin da take sauke nauyin dake wuyanta, Sin da al'ummarta na aiki tukuru wajen kara farfadowa ta hanyar gudanar da sauye-sauye a dukkanin sassan rayuwa, kama daga siyasa har zuwa hada hadar cinikayya. A daya hannun kuma, shugabancin kasar na tabbatar da daidaito, da inganta ayyukan hukumomi domin al'umma, a hannu guda suna taka rawar gani a fannin raya diflomasiyya. A wannan lokaci na rashin tabbas, Sin ta aza wani tubali na aiwatar da manufofi, wadanda za su haifar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaba.

1. An sanya tunanin shugaba Xi a kundin tsarin mulkin kasar Sin.

A watan Maris na shekarar 2018 ne majalissar wakilan jama'a ta NPC, ta amince da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar Sin, aikin da ya kasance irinsa na farko a cikin shekaru 14. Daya daga muhimman gyare gyare da aka yi a kundin a shekarar 2018, shi ne sanya tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping game da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na Sin a sabon zamani da ake ciki, cikin kundin na tsarin mulkin kasar Sin.

Wannan gyara ya sanya tunanin shugaba Xi yin kusanci da na Markisanci da tunanin Lenin, da tunanin Mao Zedong, da tunanin Deng Xiaoping, wato tunanin wakilai uku, da mahangar kimiyya game da ci gaba, a matsayin hanyoyin gudanar da tsarin mulkin kwaminisanci da JKS ke bi.

2. An zabi sabbin jagororin kasar Sin; Shugaba Xi Jinping ya yi rantsuwar kama aiki a karon farko.

Yayin taro na 13 na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta NPC, wanda ya gudana a watan Maris, an zabi shugabannin kasar Sin, ciki hadda shugaban kasar, da kuma jagororin hukumar ba da shawara kan harkokin siyasa ta JKS– da 'yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin.

A ranar 17 ga watan na Maris, aka zabi shugaba Xi Jinping a matsayin shugaban kasar Sin a sabon zagaye, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartaswa ta rundunar sojojin kasar Sin.

A wannan rana, shugaba Xi ya yi rantsuwar martaba kundin tsarin mulkin kasar Sin a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing. Wannan ne karon farko da wani shugaban kasar Sin ya yi rantsuwar kama aiki gabanin darewa karagar mulki.

3. Sin ta yi bikin cika shekaru 40 da fara aiwatar da sauye sauye da bude kofa.

A bana ne kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 40, da fara aiwatar da manufar yin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, matakin da ya sauya akalar kasar daga babbar kasa mai dogaro da noma, zuwa kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. An gudanar da babban bikin ne a watan Disamba a birnin Beijing. Yayin bikin, shugaba Xi ya jaddada gudanar da sauye sauye, da kara bude kofa ga kasashen waje a matsayin hanyar kaiwa ga kyakkyawar makomar kasar Sin ta zamani, wanda kuma zai dada daga martabar salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na kasar. Ya ce wadannan muhimman manufofi sun taka rawar gani, wajen cimma nasarorin da kasar ta sanya gaba cikin shekaru 100, da ma burinta na kara farfadowa. A daya hannun an karrama Sinawa 100 da lambobin bajimta, bisa gudummawarsu a fagen bunkasa wannan manufa, kana wasu 'yan kasashen waje 10 su ma sun samu lambobin yabo, na kawance bisa kwazonsu na yayata manufofin sauye sauye da bude kofa na kasar Sin.

4. JKS ta kara zurfafa gyare-gyare ga jam'iyyar da hukumomin gwamnati.

Yayin zaman taro na uku na kwamitin kolin JKS na 19, an bayyana cimma matsaya game da zurfafa gyare-gyare ga JKS, da hukumomin gwamnati. Manufar sauye-sauyen ita ce zamanantar da tsarin ayyukan gwamnatin kasar Sin, da inganta kwarewar aiki bisa mahanga mai inganci, wadda za ta dace da burikan da ake fatan cimmawa a nan gaba. Kwanaki biyu bayan bayyana hakan, sai aka kaddamar da sabuwar hukumar yaki da cin hanci, wato hukumar kasa mai sanya ido. Cikin watanni biyu kacal, ma'aikatu da hukumomi 25 suka kammala aikin sauye-sauye bisa tanajin tsarin mulki, aka kuma kaddamar da su bisa shawarar da aka zartas.

5. Kasar Sin ta lashi takwabin kara taimakawa kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yayin da ya jagoranci taron karawa juna sani game da kamfanoni masu zaman kansu da ya gudana a watan Nuwamba cewa, kamfanoni masu zaman kansu sun ba da gagarumar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Inda ya bukaci da a aiwatar da manufofi da matakai a fannoni 6 domin samar da yanayin da ya dace na bunkasa kamfanoni masu zaman kansu da ma yadda za a magance matsalolin da suke fuskanta. Bayan kiran da shugaban ya yi, gwamnati ta bullo da jerin manufofi da za su taimakawa kamfanoni masu zaman kansu.

6. Ayyukan diflomasiyar da kasar Sin ta samu nasara.

A shekarar 2018 mai shirin karewa Kasar Sin ta kasance mai goyon bayan tsarin dunkulewar duniya da yin cinikayya tsakanin bangarori ta daban-daban. Haka kuma kasar ta yi nasarar karbar bakuncin tarukan manyan jami'an diflomasiya, da sauran manyan tarukan kasa da kasa: da taron dandalin shekara-shekara na Boao na yankin Asiya da ya gudana a watan Afrilu, da taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai da aka gudanar a watan Yuni a Qindao, da taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2018 a birnin Beijing cikin watan Satumba da taron kolin kasa da kasa na farko na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin a watan Nuwamba a birnin Shanghai.

Taron na FOCAC wanda kasashen Afirka 54 suka halarta, ya kasance taron da ya hallara manyan jami'an diflomasiya da dama da kasar Sin ta taba karbar bakunci. Manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama ta kara samun karbuwa da ma yadda ake yayatata yayin tarukan manyan jami'an diflomasiya har ma a ziyarar da shugaba Xi ya kai kasashen waje. Shugaba Xi ya yi nasarar ziyartar kasashe 13 a yankunan Asiya da Afirka da Turai da Latin Amurka da Oceania. Haka kuma kasar Sin ta kulla huldar diflomasiya da jamhuriyar Dominica da Burkina Faso da El Salvador.

7. Xi ya ziyarci sojojin ruwan kasar dake yankin tekun kudancin Sin.

A ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2018 ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ziyarci dakarun ruwan 'yantar da al'umma ta kasar Sin dake yankin tekun kudancin kasar. Wannan ita ce runduna irinta mafi girma tun lokacin da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949. A shekarar 2018, rundunar PLA ta aiwatar da tunanin Xi na gina rundunar soja da babu kamarta a sabon zamani da ake ciki. Bugu da kari, PLA ta dukufa wajen kare tutar kasar Sin da harba bindigar gaisuwa, tun daga ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara, yayin da rundunar 'yan sandan kasar aka umarce ta kare hadadden shugabancin JKS da rundunar askarawar kasar. A ranar 13 ga watan Mayu ne, jirgin saman kasar Sin na farko da kasar ta kera ya fara tashin gwaji. Wata guda gabanin haka, sabuwar ma'aikatar kula da 'yan mazan jiya ta fara aiki.

8. Kasar Sin za ta bunkasa aikin raya tattalin arziki maras gurbata muhalli a yankin kogin Yangtze.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada yayin wani taro, bayan da ya duba yadda ake kula da muhalli da yadda ake aikin gini a yankin kogin Yangtze a ranar 26 ga watan Afrilu cewa, wajibi ne a ba da muhimmanci ga kiyaye muhalli yayin da ake raya yankin tattalin arziki na kogin Yangtze. Akwai bukatar a yi amfani da kimiya da kuma raya tattalin arziki a yankin kogin yadda ya kamata. Ya ce manufar ita ce, raya yankin tattalin arziki mai cike da kyan gani ba tare da cunkoson ababen hawa na. A farkon watan Mayu ne aka gudanar da taron kare muhalli na kasa,a lokacin ne kuma shugaba Xi ya lashi takwabin cewa, kasar Sin za ta yi yaki da matsalar hayaki mai gurbata muhalli da inganta yanayin muhallin halittu ta yadda zai dace da zamani.

9. Kasar Sin ta fito da sabon tsarin haraji da karin matakan inganta rayuwar jama'a.

A ranar 31 ga watan Agusta ne, kasar Sin ta amince da dokar biyan haraji da aka yiwa gyaran fuska a hukumance, dokar da ta kunshi manyan gyare-gyare a fannoni kamar na kudaden da za a biya haraji, rukunin da suka fada cikin biyan haraji, da wadanda aka tsame daga biyan haraji, da rukunin da za a yiwa rangwamen haraji. Dokar da aka yiwa gyaran fuska ta taimaka wajen rage nauyi kan masu biyan haraji.

Haka kuma kasar Sin ta bullo da jerin matakai na inganta rayuwar jama'a. A ranar 1 ga watan Yuli ne, majalisar gudanarwar kasar ta sanar da cewa, za a kafa wata gidauniya da za ta rika kula da kudaden fansho a yankunan daban-daban, matakin da zai taimaka wajen tabbatar da ganin an biya ma'aikatan da suka yi ritaya a kan lokaci. Ya zuwa karshen watan Satumba, mutane miliyan 46.199 ne suka amfana da alawus-alawus din da ake baiwa mazauna karkara da birane, mazauna birane da aka tantance ya karu da kaso 7.6 cikin 100 yayin mazauna kauyuka da suka amfana da shirin da aka tantance ya kai kaso 12.9 cikin 100.

A ranar 1 ga watan Oktoba, sabon tsarin tsugunar da jama'a da tuni ya fara aiki, zai taimakawa yara masu nakasa, wajen biya musu kudaden magani. Daga bisani a cikin watan, a ranar 10 ga watan Oktoba, an kara sanya yara 17 masu fama da cutar sankara cikin tsarin inshoran magani, don taimakawa masu fama da cutar sankara.

10. Kasar Sin ta tsaurara dokoki kan kamfanonin hada magungunan riga kafi.

A watan Yuli ne, aka gano cewa, babban kamfanin hada alluran riga kafi, mai suna Changsheng Bio-technology Co. dake Changchun a lardin Jilin ya jirkita muhimman bayanan samar da alluran da yake yi, sannan ya rika samar da alluran riga kafi marasa inganci.

Shugaba Xi ya ba da umarni a gudanar da cikakken bincike game da wannan lamari kana a zartar da hukunci mai tsanani kan wadanda aka samu da laifi. An dai kama mutane da dama a kamfanin, sannan aka ci tarar kamfanin Yuan biliyan 9.1, kwatankwacin dala miliyan 1.3.

Sakamakon wannan badakala, masu tsara dokoki a kasar Sin sun tsaurara dokoki kan kamfanonin harhada alluran rigakafi. A ranar 16 ga watan Oktoba, an sanar da wani tsari na biyan diyya ga wadanda alluran rigakafin ta yiwa illa, inda aka kebe wasu kudade na musamman don biyan diyya. A ranar 11 ga watan Nuwanba an gabatarwa zaman zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a da aka saba yi bayan watanni bibbiyu wani sabon daftarin doka, inda aka yi kira da a sa-ido sosai kan yadda ake hada alluran riga kafi, da bincike da ma yadda ake raba alluran.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China