Za a yi taron tattauna harkokin cinikayya tsakanin manyan jami'an Sin da na Amurka a tsakanin ranekun 14 da 15 ga watan Fabrairu a Beijing
Daga ranar 14 zuwa ta 15 ga wata, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, mataimakin firaministan kasar Sin, kana wakilin Sin dake kula da shawarwari tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki, Liu He zai yi wani sabon zagayen tattaunawa da wakilin ciniki na kasar Amurka Robert Lighthizer da ministan harkokin kudin Amurka Steven Mnuchin, kan harkokin tattalin arziki da ciniki dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku