Rahotannin na cewa, a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da takwaransa na kasar Hungary Peter Szijjarto ke ganawa da manema labarai, Pompeo ya ce idan Hungary ta girke na'urorin sadarwar kamfanin Huawei na kasar Sin, hakan na iya shafar hadin-gwiwar Amurka da Hungary. Amma ministan harkokin wajen Hungary ya ce, hadin-gwiwar da kasarsa ke yi da kasar Sin sam ba zai lalata dangantakarta da Amurka ba.
Game da wannan batu, Hua Chunying ta ce, Sin ta yabawa wannan ra'ayi na ministan harkokin wajen Hungary, haka kuma tana fatan bangarori daban-daban za su yi kokarin kirkiro wani kyakkyawan yanayi na nuna adalci da fahimtar juna ga hadin-gwiwar kasashen duniya.(Murtala Zhang)