in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya ce babu wata kasa da take da karfin "sake gina" kasar Sin
2018-10-10 20:49:01 cri
Yau Laraba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya maida martani game da kalaman shugaban kasar Amurka dangane da "sake gina" kasar Sin, inda ya ce, wasu na maganar cewa, wai saboda kasar Amurka ce kasar Sin ta samu dimbin nasarori, wannan ba gaskiya ba ne sam. Kasar Sin ba za ta dogaro kan taimako ko tallafin wasu kasashe ba don samun bunkasuwa, kana kuma, a duk fadin duniya, babu wata kasa wadda ke da karfi na "sake gina" kasar Sin.

Wasu rahotannin da aka ruwaito na cewa, shugaban Amurka ya sha bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, gibin cinikayya dake tsakanin Amurka da Sin ya sa Sin ta samu dimbin kudade, al'amarin da ya nuna cewa, Amurka ce ta "sake gina" kasar ta Sin. Game da furucin nasa, Lu Kang ya ce, akwai dalilai da dama wadanda suka jawo gibin cinikayya tsakanin kasashen biyu. Amurka ta sayo abubuwa masu yawa daga kasar Sin, amma ba ta sayar da abubuwa da yawa zuwa kasar Sin ba, kana kuma ta gindaya wasu sharudda game fitar da nau'o'in kayayyakin da ake samun riba mai tsoka zuwa kasar Sin, abun da ya jawo gibin cinikayya tsakanin Amurka da Sin. Amma idan har saboda wannan ne kawai Amurka ta zargi kasar Sin, to wannan ba adalci ba ne.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China