Bangarorin biyu sun yi kokarin aiwatar da ra'ayi iri daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma tare, da zurfafa mu'amala da musanyar ra'ayi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi kasuwanci da tsare-tsare, da kara samun fahimtar juna, da aza tubali mai inganci ga warware matsalolin da suka jawo hankalinsu dukka. Bangarorin biyu sun kuma amince za su ci gaba da kara yin mu'amala da juna.(Murtala Zhang)