in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a gudanar da shawarwari kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka
2019-01-04 14:08:44 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a yau Jumma'a cewa, Sin da Amurka za su gudanar da shawarwari tsakanin mataimakan ministocinsu kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya daga ranar 7 zuwa 8 ga wata.

Kakakin ya ce, da safiyar yau Jumma'a, mataimakan ministocin Sin da Amurka sun zanta ta waya, inda suka tabbatar da cewa, mataimakin wakilin Amurka kan harkokin cinikayya Jeffrey Gerrish zai kawo ziyara kasar Sin a ranakun 7 da 8 ga wata, inda tawagarsa za ta yi shawarwari da tattaunawa tare da rukunin kasar Sin game da ayyukan aiwatar da muhimman ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a kasar Argentina.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China