in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da jadawalin sake karfafa taimakawa bangarori masu zaman kansu
2019-02-15 10:12:15 cri
Kasar Sin ta wallafa wani jadawalin karfafa taimakon kudi ga bangarori masu zaman kansu.

Babban ofishin kwamitin tsakiya na JKS da babban ofishin gudanarwar kasar ne suka fitar da jadawalin.

A cewar daftarin, ya kamata a dauki dabarun tafiyar da harkokin kudi da na ba da rance daban-daban, sannan a karfafawa cibiyoyin hada-hadar kudi gwiwar bada karin rance ga kamfanoni masu zaman kansu da kanana da matsakaitan kasuwanci.

Daftarin ya bayyana cewa, idan suka cimma wasu ka'idoji, kamfanoni masu zaman kansu za su iya fadada hanyar samun rance kai tsaye, sannan za a mara masu baya wajen bayar da takardun lamuni. Har ila yau, ya ce ya kamata cibiyoyin hada-hadar kudi su sanya jari cikin takardun lamunin da kamfanoni masu zaman kansu suka bayar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China