in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Bangaren mai da iskar gas na kasar Sin zai inganta ayyukansa a shekarar 2019
2019-01-23 13:14:37 cri
Wani rahoto da hukumar kula da harkokin makamashi da jigilar kayayyaki ta ruwa DNV GL ta fitar, na nuna cewa, bangaren mai da iskar gas na kasar Sin zai kara daukar matakan rage tasirin yanayi kan ayyukan da yake gudanarwa a sabuwar shekarar 2019.

Sabon binciken ya nuna cewa, kaso 61 cikin 100 na manyan masana harkar mai da iskar gas a kasar ta Sin sun bayyana cewa, kungiyoyinsu sun dukufa wajen karkata ga amfani da makamashin da ba ya fitar da abubuwan dake gurbata muhalli, idan aka kwatanta da kaso 51 cikin 100 dake da wannan ra'ayi a duniya baki daya.

Bugu da kari, nan da shekarar 2020 shugabannin kamfanonin kasar Sin za su kara mayar da hankali wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da a kalla kaso 15 cikin 100 cikin matakan da aka tsara a shekarar 2015.

Rahoton hukumar ya kuma nuna cewa, wasu karin rukunin kamfanonin mai da iskar gas a sassan kasar Sin na kokarin ganin sun aiwatar da manufar gwamnati game da kiyaye gurbatar mahalli. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China