in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzkin kasar Sin ya bunkasa da kaso 6.6 cikin 100 a shekarar 2018
2019-01-21 13:38:18 cri
Alkaluman da hukumar kidiggar kasar Sin(NBS) ta fitar a yau Litinin na nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kaso 6.6 cikin 100 a shekarar 2018, sama da hasashen da mahukuntan kasar suka yi na samun kimanin kaso 6.5 cikin 100.

Shugaban hukumar ta NBS Ning Jizhe shi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai. Ya ce, tattalin arzikin kasar ya bunkasa cikin yanayin da ya dace a shekarar ta 2018, inda ci gabansa baki daya ya kasance cikin daidaito kana ya samu bunkasar da ake bukata.

Ning ya ce, tattalin arzikin kasar ta Sin ya kuma ba da gudummawar kaso 30 cikin 100 ga bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, ya kuma kasance wanda ke kan gaba wajen ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, GDPn kasar ya kai Yuan Triliyan 90,0309, kwatankwacin dalar Amurka Triliyan 13.28, inda bangaren samar da hidima ya dauki sama da rabin wannan adadi.

Alkaluman hukumar ta NBS sun kuma suna cewa, a shekarar 2018 jarin kadarorin kasar ya karu da kaso 5.9 cikin 100 kasa da karuwar kaso 7.2 cikin 100 a shekarar 2017.

Haka kuma, bangaren masana'antun kasar ya samu karuwar kaso 6.2 cikin 100 a shekarar da ta gabata bisa makamancin lokaci na bara, ragu da kaso 0.4 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China