in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da sabon zagayen tattaunawa kan batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka a Beijing
2019-02-14 09:45:18 cri

A yau Alhamis da safe, Mr. Liu He, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar, sannan jagoran bangaren Sin kan tattaunawa game da batun tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni, da Mr. Robert Lighthizer, wakilin cinikayya na Amurka da Steven Mnuchin, ministan kudin Amurka su uku sun shugabanci bikin kaddamar da taron tattaunawa kan batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.

Bisa ajandar da aka kafa, za a yi wannan zagayen tattaunawa ne tsakanin ranar 14 da 15 ga wannan watan na Fabrairu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China