in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bincike: Kamfanonin kasar Sin dake sassan duniya na samun yabo
2019-01-23 10:03:36 cri
Wani rahoton bincike na kasa da kasa da aka fitar a jiya Talata, na nuna cewa, galibin jama'a a duniya na yabawa kamfanonin kasar Sin dake gudanar da ayyukan raya kasa a kasashen ketare, duba da yadda suka kasance a sahun gaba a fannin kirkire-kirkire a duniya.

Rahoton mai taken "Yadda ake kallon kamfanonin kasar Sin a duniya" wanda kamfanin ba da shawarwari mai suna Brunswick ya wallafa, ya tattara bayanansa ne kan binciken da ya gudanar a kasashe 18 da kamfanonin kasar Sin suke da jari da ma shirye-shirye, da kuma hirarraki da ya gudanar da manyan shugabannin kamfanonin kasar Sin 300 dake gudanar da ayyukansu a kasashen ketare ko kuma suke da shirin yin haka.

Kamfani ya gudanar da wannan bincike ne daga watan Oktoba zuwa Nuwamban da ya gabata a kasashe da suka hada da Amurka da Burtaniya da Jamus da Singapore. Sauran sun hada da Malaysia da Indonesia da Najeriya da Kenya da Kazakhstan da kuma Hungary.

A cewar rahoton, shugabannin 'yan kasuwan kasar Sin na ganin cewa, yadda kamfanonin kasar suka fadada harkokinsu zuwa kasashen ketare, shi ne kashin bayan dorewar ci gabansu.

Haka kuma a yayin da suke amfani da damar kara sayar da hajojinsu a kasuwannin cikin gida, kamfanonin na kara zakulo karin damammaki, inda rahotanni ke cewa, a shekarar da ta gabata kaso 49 cikin 100 na kayayyakin da kasar ke fitarwa da wadanda take sayarwa sun kasance masu matukar muhimmanci. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China