Tattalin arzikin Sin ya bunkasa da kashi 6.6 bisa 100 a shekarar 2018
2019-01-21 10:56:02
cri
Wasu alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin NBS ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa da kashi 6.6 bisa 100 a shekarar 2018, inda ya dara hasashen da mahukuntan kasar suka yi na yiwuwar samun bunkasuwar tattalin arzikin da kashi 6.5 bisa 100. (Ahmad)