in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu: MDD jigo ce wajen yaki da ayyukan ta'addanci
2019-02-12 11:33:21 cri

Wani babban jami'in diplomasiyyar kasar Afrika ta kudu ya bayyana jiya Litinin, cewar bisa ga yadda ayyukanta suka fadada a duniya, MDD ta kasance jigo wajen tafiyar da ayyukan yaki da ta'addanci na kasa da kasa.

Jerry Matjila, wakilin din din din na kasar Afrika ta kudu a MDD, shi ne ya bayyana hakan ga kwamitin sulhun MDD, inda ya buga misali da kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta ISIL. Ya kara da cewa, "Muhimmancin da take bayarwa ga kasashe mambobinta wajen shawo kan kalubalolin dake addabarsu game da yaki da kungiyar ISIL ba zai taba misaltuwa ba."

Ya kuma nuna cewa, yaki da kungiyar lSIL yana bukatar dabaru, da ingantaccen shiri, wanda ya kunshi tsarin hadin gwiwa daga cikin gida, da hulda a tsakanin kasa da kasa, da matakin shiyya-shiyya da kuma matakin kasa da kasa, wanda ya kunshi musayar bayanai da kwarewa.

Ya ce, kasar Afrika ta kudu a ko da yaushe a shirye take wajen tallafawa dukkan shirye shiryen yaki da ayyukan ta'addanci.

Jami'in diplomasiyyar na Afrika ta kudu ya kara da cewa, daukar matakai na tsaro kadai ba za su wadatar ba wajen samun nasarar dakile barazanar ta'addanci, daukar matakan rigakafin faruwa matsalar shi ne abu mafi muhimmanci.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China