in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afrika ta kudu ta shiryawa jan hankalin karin Sinawa masu yawon bude ido
2019-02-04 11:53:33 cri
Kasar Afrika ta kudu, ta ce a shirye take ta kara jan hankalin Sinawa masu ziyarar kasar, inda ta ce tana kokarin saukaka musu tafiya zuwa kasar, ta yadda za su ji dadinta.

Ministan kula da harkokin yawon bude ido na kasar, Derek Hanekom, ya bayyana yayin bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da aka gudanar a ofishin jakadancin Sin dake Afrika ta kudu cewa, a kowace shekara, a kan samu Sinawa 100,000 dake zuwa yawon bude ido a kasar, yana mai cewa za su iya kara yawan adadin.

A 2018 ne kasashen Afrika ta kudu da Sin, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wadda ta kunshi saukakawa Sinawa 'yan kasuwa da masu yawon bude ido samun biza domin bunkasa bangaren yawon bude ido.

Derek Hanekom ya ce wannan na daya daga cikin matakan da aka dauka na saukakawa Sinawa matafiya samun bizar zuwa Afrika ta kudu.

Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa na dubu yuwuwar bada bizar shekaru 10 mai damar shige da fice sau da dama, da kuma samun bizar ta na'ura ga Sinawa masu yawon bude ido. Haka zalika, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar na duba yuwuar lura da wasu bizar dake cikin fasfon Sinawa, kamar bizar Schengen da ta Amurka ko Australia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China