in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta kudu ya sha alwashin tabbatar da nasarar sulhunta 'yan kasar sa
2018-12-17 10:36:43 cri
Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya sha alwashin tabbatar da nasarar sulhunta 'yan kasar sa, ta hanyar kawo karshen halayyar nuna fifiko, da nuna isa, da maida wasu sassa saniyar ware.

Mr. Ramaphosa ya bayyana hakan ne a garin Mthatha, dake gabashin lardin Cape, yayin taron gangamin ranar sulhu ta kasar, wadda ake bikin kewayowar ta a duk ranar 16 ga watan Disamba, tun daga shekarar 1994 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar.

Wannan rana dai na da matukar muhimmanci ga 'yan Afirka ta kudu, duba da yadda ake amfani da zagayowar ta, wajen ingiza batutuwan da suka shafi sulhu, da hada kan 'yan kasar wuri guda.

Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Ramaphosa ya ce, ya zama wajibi al'ummar nahiyar Afirka su hade kai wuri guda, wajen yaki da masu amfani da miyagun kalaman nuna kiyayya ga bakaken fata, da bakaken fata masu rajin hallaka fararen fata, da ma duk wadanda ke aibata wasu saboda banbancin addini, ko al'adu ko yare.

Kaza lika shugaba Ramaphosa ya ce, ba za a samu cikakkiyar biyan bukata ba, har sai an hada batun sulhu da bunkasa tattalin arziki. Don haka gwamnatin sa za ta kara azama, wajen fadada ba da horo a fannonin koyar da sana'o'in hannu, da samar da dama ga 'ya'yan talakawa, ta yadda za su iya kaiwa ga manyan makarantu na zurfafa ilimi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China