Ban da wannan kuma, Hua ta ce, wannan matakin da Amurka ta dauka ko kadan ba shi da ma'ana, zai kuma lahanta zaman lafiya da tsaron shiyya-shiyya, da kawo tasiri ga yunkurin kwace damarar makaman nukiliya, da kuma tayar da gasar jan damara, hakan zai kawo illa ga daidaito da zaman karko a duk fadin duniya.
Hua ta kuma kara da cewa, kullum kasar Sin na tsayawa kan warware matsalar yaduwar makamai masu linzami ta hanyar diplomasiyya kuma a siyasance, da kuma nuna adawa ga hanyar neman tsaro bisa tushen lalata moriyar sauran kasashe.
Baya ga haka, Hua ta ce, Sin zata tsaya kan bin hanyar neman ci gaba cikin lumana, da tsayawa kan manufar tsaron kasa irin ta kare kai, "bata da ra'ayi kuma ba zata kawo barazana ga kasashen duniya ba, ciki har da Amurka." (Bilkisu)