in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar wajen Sin ya yi jawabi game da cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka
2018-12-30 17:30:39 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya yi jawabi game da cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka a yau 30 ga wata.

A cikin jawabinsa, Lu Kang ya bayyana cewa, shekarar 2019 shekara ce ta cika shekaru 40 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka. A cikin shekarun 40, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, an samu ci gaba kan hadin gwiwar dake tsakaninsu. Kafin shekaru 40 da suka gabata, yawan mutanen dake zirga zirga a tsakanin Sin da Amurka bai wuce dubu goma ba a kowace shekara, amma a shekarar 2017, yawansu ya kai miliyan 5 da dubu 300. Kafin shekaru 40 da suka gabata, yawan cinikin da aka yi a tsakanin Sin da Amurka bai wuce dala biliyan 2.5 ba, amma a shekarar 2017, yawansu ya kai fiye da biliyan 580. Kafin shekaru 40 da suka gabata, ba a zuba jari ga juna a tsakanin Sin da Amurka ba, amma yawan jarin da aka zuba a tsakanin kasashen biyu a shekarar 2017 ya kai fiye da dala biliyan 230. A cikin shekaru 40 da suka gabata, an yi hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakanin Sin da Amurka, har ma ga dukkan yankunan duniya baki daya.

Lu Kang ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka domin tabbatar da matsaya guda da shugabannin Sin da Amurka suka cimma a lokacin ganawarsu a kasar Argentina, da fadada hadin gwiwa bisa tushen samun moriyar juna, da daidaita matsalolinsu bisa tushen girmama juna, da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka bisa tushen yin hadin gwiwa, da kiyaye zaman lafiya, don kara amfanawa jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar dukkan kasashen duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China