Jiya Alhamis ranar 31 ga watan Janairu bisa agogon wurin, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, wanda ya jagoranci tawagar Sin zuwa Amurka don sabon zagaye na babban shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu.
Yayin ganawar, da farko dai Liu He ya mika sakon da Shugaba Xi Jinping ya aikewa takwaransa Trump, inda Xi ya bayyana cewa, a watan da ya gabata, shi da shugaba Trump sun gana cikin nasara a kasar Argentina, inda suka amince da raya huldar da ke tsakanin Sin da Amurka bisa ka'idojin hadin kai da tabbatar da daidaito da ma kwanciyar hankali. Kuma bisa ra'ayin bai daya da suka cimma, tawagogin tattalin arziki na kasashen biyu sun yi jerin shawarwari a tsakaninsu, sa'an nan sun samu babban ci gaba.
Ban da wannan, Liu He ya ce, a cikin tattaunawar ta wannan zagaye, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi sosai kan samun daidaiton cinikayya, musanyar fasahohi, kiyaye hakkin mallakar ilimi da dai sauran fannoni, sa'an nan sun samu babban ci gaba, lamarin da ya aza harsashi mai inganci ga tattaunawa ta gaba.
A nasa bangaren, Shugaba Trump ya furta cewa, an samu ci gaba sosai a cikin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a wannan zagaye. Inda ya ce ya na fata bangarorin biyu za su cimma wata babbar yarjejeniya, wadda za ta ba da muhimmiyar ma'ana ga kasashen biyu da ma duk duniya baki daya.(Kande Gao)