in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi alkawarin kara kokarin yaki da cin hanci da rashawa
2019-02-06 16:06:29 cri
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya furta a jiya Talata cewa, ko da yake aikin yaki da cin hanci da rashawa da ake gudanarwa a Najeriya na gamuwa da kalubale, amma duk da haka, ya yi alkawarin muddin ya ci zaben shugabancin kasar da zai gudana a ranar 16 ga watan da muke ciki, zai ci gaba da kokarinsa, na neman kau da cin hanci da rashawa daga kasar.

Shugaban ya yi wannan furucin ne, a wajen wani bikin kamfen da aka yi a Ado-Ekiti dake kudancin kasar Najeriya, inda ya ce gwamnatinsa, na ta kokarin dakile cin hanci da rashawa, sai dai aikin na cikin wani hali mai wuya. Duk da haka, shugaba Buhari ya yi kira ga wadanda za su jefa kuri'a a yayin zaben, da su nuna masa goyon baya.

Ya ce yana da cikakken imani kan cika alkawarin da ya dauka a shekarar 2015, wato kau da cin hanci da rashawa tun daga tushensa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China